June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

shugaban kasa Buhari ya aike da sakon ta ya murna ga sabon shugaban kungiyar lauyoyi Mr Olumide Akpata

1 min read

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon taya murna ga sabon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa Mr Olumide Akpata wanda ya samu nasarar lashe zaben shugabancin kungiyar a baya bayan nan.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Mr Femi Adesina ya fitar a yau Asabar.
Sanarwar ta bayyana sabon shugaban a matsayin wanda ya riki kungiyar tsahon shekaru biyu tare da fito da dabarun ciyar da ita gaba.
Kazalika sanarwar ta bukaci Mr Olumide da ya ci gaba da ayyukan tafiyar da kungiyar cikin tsari tare da sanya al’amuran gwamnati a kowanne mataki don samun shawarwarin da ya kamata don ciyar da kungiyar gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *