July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu daga jami’ai na sun ci amanar da na ba su – Buhari

1 min read

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce wasu daga
cikin jami’an da ya baiwa shugabancin hukumomin kasar
sun ci amanar da ya basu. Buhari ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a
Abuja, bayan gudanar da Sallar idi a jiya Juma’a, inda ya sha
alwashin gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yiwa
shugabanni da manyan jami’an wasu daga cikin hukumomin
gwamnatinsa da suka hada da NDDC da kuma EFCC.
Karo na farko kenan da shugaban Najeriyar yayi tsokaci kan binciken
almundahanar makudan kudade da kadarorin da aka bankado a
hukumar raya yankin Niger Delta NDDC dake karkashin tsohon
gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio, da kuma hukumar yakar
rashawa EFCC da aka dakatar da mukaddashin shugabanta Ibrahim
Magu, da aka zarga da karkatar da makudan kudaden da satar da aka
kwato, zargin da yake ci gaba da musantawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *