June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Mata 7 Sun Mutu a Wani Shagon Gyaran Gashi

1 min read

Hukumomi a jihar Neja a Nigeria
sun kaddamar da bincike don gano dalilin mutuwar
wasu ‘yan mata guda 7 da sanyin safiyar ranar juma’a
31 ga watan Yuli, a daidai lokacin da ake shirin idin
Babbar Sallah.
Wannan al’amari dai ya faru ne a garin Rijau da ke
jihar Neja, bayanai sun nuna cewa ‘yan matan su 6 sun
je wani shago ne da ake gyran gashi domin yin kitson
sallah amma daga bisani sai dai aka ga gawarwakinsu
tare da mai gyaran gashin. Uku daga cikin ‘yan matan
daga iyali daya suka fito.
Shugaban karamar hukumar Rijau Honarabul Bello
Bako, ya ce ya bada umurnin a yi wa yaran jana’iza
kafin daga bisani a ci gaba da bincike, yayin da daya
daga cikin iyayen yaran Alhaji Abdulrazak Rijau, ya ce
iya abinda ya sani shi ne yaran sun tafi kitso, kawai sai
dai aka kira shi aka fada masa abinda ya faru.
Rudunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar
lamarin inda kakakin ‘yan sandan jihar ASP Wasiu
Abiodun ya ce suna kan binciken lamarin.
Gwamnatin jihar Neja, a ta bakin sakatarenta Ahmed
Ibrahim Matane, ta bayyana lamarin a matsayin “mai
tayar da hankali” ta kuma jajanta wa iyalan mamatan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *