June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kama wani babban dillalin miyagun ƙwayoyi

1 min read

Jami’an tsaro a Mexico sun ce sun kama wani shugaban gungun masu
safarar miyagun ƙwayoyi a jihar Guanajuato da ke tsakiyar ƙasar.
Gwamnan jihar ta Guanajuato ya ce wanda aka kama mai suna Antonio
Yepez wanda aka fi sani da “El Marro,” wasu jami’an haɗin gwiwa ne
suka damƙe shi a ranar Lahadi.
Kafofin watsa labarai na ƙasar na nuna hotunan wani mutum da aka
rufe wa ido da adiko tare da jami’an tsaro ɗauke da makamai.
Ana dai zargin El Marro da satar mai, kuma ana nemansa kan laifuka
da dama a jihar Guanajuato.
Wannan kamen da aka yi masa na zuwa ne makonni kaɗan bayan ‘yan
sanda sun kama maahifiyarsa da kuma ‘yar uwarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *