June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Boko Haram’ ta kashe mutum 13.

1 min read

Wasu da ake zargin ‘yan ƙunigiyar Boko Haram ne sun kashe akalla
mutum 13 a Kamaru tare da raunata mutum takwas a wani hari da ake
zargin ƙungiyar ta kai a arewacin ƙasar a ranar Lahadi.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa maharan sun
jefa gurneti ga wasu rukunin mutane da ke zauna a wani sansanin ‘yan
gudun hijira a Mozogo da ke kusa da iyakar Najeriya, in ji Medjeweh
Boukar, wani magajin gari a ƙasar.
Wani jami’in tsaro wanda ya tabbatar da kai harin ya ce cikin waɗanda
suka samu rauni biyu sun sake mutuwa wanda yanzu adadin waɗanda
suka mutu ya kai 15.
Ƙungiyar Boko Haram dai ta shafe sama da shekaru 10 tana ƙoƙarin
kafa daular Musulunci a Najeriya.
Rikicin da ƙungiyar ta haddasa ya yi sanadin mutuwar sama da mutum
30,000 tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.
Rikicin ƙungiyar ya faɗaɗa zuwa makwaftan Najeriya kamar Chad da
Nijar da Kamaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *