Corona -Zamu bude ko wani bangare baki daya.
1 min read
Gwamnan jihar Lagos ya sanar
da cewa za a bude Majami’u da Masallatai don jama’a
su je yin ibada daga ranar 7 ga watan Agusta, ya yi
wannan bayanin ne a wurin wani taron manema
labarai a ranar Asabar 1 ga watan Agusta, a cewar wani
rahoto na kamfanin dillancin labaran Reuters.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya kuma ce za a ba
wuraren saida abinci, wuraren rawa da wuraren
shakatawa damar sake bude harkokinsu amma ba
kamar da ba daga ranar 14 ga watan Agusta, a yayin da
jihar inda cutar COVID-19 ta fi kamari ke sassauta
matakan kulle da takaita zirga-zirga duk da cewa ana ci
gaba da samun karin adadin wadanda ke kamuwa da
cutar.
Jihar Lagos, da ke da yawan al’umma miliyan 20, ta
samu adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar
coronavirus sama da 15,000 kuma mutum 192 suka
mutu, nesa ba kusa ba ita ce jihar da ke da kaso mai
yawa cikin mutum 43,537 da suka kamu da cutar a
Najeriya.
Gwamnatin jihar ta bada umurnin a rufe wurare da
yawa tare da daukar matakan kulle a watan Maris da
ya gabata don dakile cutar mai yaduwa da sauri.