July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Karin Mutum 386 Suka Kamu Da COVID-19 a Najeriya

1 min read

Adadin wadanda suka kamu da
cutar COVID-19 ya kai 43,537 a Najeriya a cewar
hukumar NCDC mai sa ido akan cututtuka masu
yaduwa a daren ranar Asabar 1 ga watan Agusta.
A sakon da take sabuntawa a duk rana a shafinta na
Twitter, hukumar NCDC ta ce an samu karin mutum
386 da suka kamu da cutar a ranar Asabar. Cikin
mutum 43,537 da suka kamu da cutar, 20,087 sun
warke yayin da wasu su 883 suka mutu.
Hukumar ta kuma ce an samu adadi mafi yawa a ranar
daga birnin tarayya Abuja inda aka samu mutum 130
sai kuma jihar Legas da ke biye da mutum 65.
Sauran jihohin sun hada da Ondo inda aka samu
mutum 37, 29 Osun, 23 Plateau, 15 Rivers, 14 Enugu, 12
Nasarawa, 11 Bayelsa, 11 Ebonyi, 9 Ekiti, 8 Oyo, 8 Edo, 6
Abia, 3 Ogun, 3 Katsina, 1 Imo, sai kuma 1 Adamawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *