Ƴan bindiga kan babura da suka addabi Arewacin Najeriya
1 min read
‘Yan bindiga masu amfani babura waɗanda ke zaune a dazukan da
aka yi biris da su na ci gaba da kai hare-hare a wasu yankuna na
arewa maso yammacin Najeriya.
‘Yan bindigar su ne na baya-bayan nan da suka shiga harkar garkuwa
da mutane domin neman kuɗin fansa inda kuma suke matsa ƙaimi a
hare-harensu.
Shekaru goma da suka wuce, an kashe sama da mutum 8,000 a
jihohin Sokoto da Kebbi da Naija da Zamfara kamar yadda ƙungiyar
nan da ke ƙoƙarin kare afkuwa da kuma sulhunta rikici ta
International Crisis Group ta bayyana. Sai dai hare-haren baya-bayan nan da aka kai a mahaifar shugaban
Najeriya wato jihar Katsina inda aka kashe sama da mutum 100
tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni sun jawo zanga-zanga inda aka
nemi shugaban ƙasar da ya yi murabus.