June 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana Najeriya: Masu cutar fiye da 22,000 ke ci gaba da jinya a ƙasar

1 min read

Mutum 304 ne waɗanda suka kamu da cutar korona hukumomin
lafiya a Najeriya suka sake ganowa ranar Lahadi, hakan dai ta sa
mutanen da cutar ta harba yanzu sun kai 43,841.
Cikin alƙaluman da take fitarwa a kullum, hukumar daƙile cutuka
masu yaɗuwa ta nuna cewa masu korona biyar sun mutu cikin sa’a
24 a ƙasar.
Sai dai saɓanin ranar Asabar,, kusan kashi ɗaya cikin uku na
mutanen da aka gano da cutar korona a Lahadin nan, suna Lagos ne
bayan tsawon kwana uku jere ana samun lafawar yaɗuwar ƙwayar
cutar.
Sai kuma Abuja, inda mutum 39 suka sake kamuwa kwana guda
bayan gano mutum 130 da cutar a babban birnin ƙasar.
Alƙaluman NCDC sun nuna cewa mutum 221 sun warke daga cutar
har ma an sallame su daga cibiyoyin kwantar da marasa lafiya don
komawa cikin iyalansu a ranar Lahadi.
Hakan ya nuna har akwai marasa lafiya 22,645 da ke kwance a
cibiyoyin killace masu cutar korona suna jinya a faɗin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *