July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnan Borneo zulum ya ce da Jami’an tsaro ake kashe al’ummar jihar.

2 min read

Gwamnan jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya ya sake nanata
cewa ƙoƙarin murƙushe ƙungiyar Boko Haram na shan zagon ƙasa
daga wani rukuni na jami’an tsaron ƙasar.
Babagana Umara Zulum ya ce ba zai iya yin shiru cikin yanayi na
kashe-kashe ba, saboda rantsuwar da ya yi tsakaninsa da Allah a kan
zai kare al’ummar jiharsa.
Wannan na zuwa ne yayin da jihar Borno ke ganin ƙaruwar hare-
haren ‘yan ta-da-ƙayar-baya, kuma ko a ranar Asabar sai da wani hari
ya kashe mutum 15 ciki har da ƙananan yara a yankin kan iyaka cikin
ƙasar Kamaru.
Gwamnan dai ya ce akwai buƙatar shugaba Muhammadu Buhari ya
san cewa zagon ƙasan da ake yi daga cikin harkar tafi da tsaro na
kawo cikas ga ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin ‘yan ta-da-ƙayar-bayan
na sama da shekara goma Babagana Zulum na jawabi ne gatse-gatse kwanaki ƙalilan bayan
kwambar motocinsa mai matuƙar tsaro kwatsam ta yanke tafiya,
kuma ya juya ya tsere daga garin Baga na kusa da Tafkin Chadi
saboda ɓarin wutar bindigogi babu ƙaƙƙautawa.
Sojoji sun ɗora alhakin abin da ya faru kan Boko Haram. Sai dai
Zulum ya nuna cewa da hannunsu cikin abin da ya faru har ya sake
amfani da kalmar “zagon ƙasa”.
Wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sada zumuntar gwamnan ta
ambato shi yana faɗa wa takwarorinsa gwamnonin APC yayin wata
ziyarar jaje ranar Lahadi cewa: “Zan ci gaba da yin tsayuwar daka,
daram kan ƙudurin cewa Allah ne kaɗai ke ba da mulki.
Ba na neman wa’adi na biyu, idan ya nufe ni da kammala wannan
ma, to na gode Allah. Amma ni a matsayina na gwamna, na yi shiru
al’umma jihar Borno miliyan shida su mutu, su ƙare, hakan ba zai
zama alheri gare ni ba.
Na yi rantsuwa tsakanina da Allah zan kasance mai gaskiya ga
al’ummata,” in ji Gwamna Zulum
Ya kuma tuhumi abin da ya sa sojojin Najeriya suka hana dubban
mutanen da rikicin ya raba da gidajensu koma wa gonakinsu a
lokacin da su sojoji ke noma a filaye.
BBC ta tuntuɓi rundunar sojin Najeriya don jin martaninta game da
waɗannan manyan zarge-zarge, amma ta ce ba ta sa-in-sa da
shugabannin siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *