July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mayakan Boko Haram sun halaka mutane 13 a arewacin Kamaru

1 min read

Majiyoyi daga hukumomin tsaron Kamaru sun ce
mayakan Boko Haram sun halaka akalla mutane 13 tare
da jikkata wasu 8, Yayin farmakin da suka kai da bama
baman gurneti kan kauyen geshewa a arewacin kasar. Magajin garin Mozogo inda aka kai farmakin, a yankin na arewa mai
nisa, Medjeweh Boukar, yace gungun mayakan na Boko Haram da ba
a tantance yawansu ba sun farwa wani sansanin yan gudun hijira
dake kauyen Geshewe a gaf da iyakar Najeriya inda suka jefa bama
baman gurneti cikin taron jama’a.
Sai dai daga bisani wani jami’in tsaro ya ce adadin rayukan da suka
salwanta a farmakin ya karu zuwa 15, bayan mutuwar biyu daga cikin
mutanen da suka jikkata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *