July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Nema takai kayan a gaji Adamawa da Taraba

2 min read

A daidai lokacin da jama’a a
Najeriya ke ci gaba da kokawa game da matsalolin
rayuwa, musamman abinci, hukumar kai agajin
gaggawa NEMA ta kai dauki ga ‘yan gudun hijira
wadanda tashe-tashen hankulan Boko Haram da kuma
fadace-fadacen kabilanci ya shafa a jihohin Adamawa
da Taraba.
Ya zuwa yanzu akwai ‘yan gudun hijira dubu uku da
dari tara da talatin da shida (3,936) a sansanonin
Malkohi, St. Theresa da kuma Fufore wadanda rikicin
Boko Haram ya raba su da gidajen su a jihar Adamawa.
Hukumar ta NEMA, wadda ke kula da sansanonin ‘yan
gudun hijira ta ce, za ta ci gaba da kai tallafin abinci ga
‘yan gudun hijirar a duk wata, a cewar jami’in
hukumar NEMA Mallam Abubakar Sadik Nuhu, wanda
shi ya jagoranci raba kayyakin abincin a sansanin ‘yan
gudun hijira dake Fufore.
Daya daga cikin shugabanin ‘yan gudun hijira a
sansanin na Fufore, Bakura Umar Mika ya ce, suna kira
ga gwamnati da ta taimaka musu da wurin zama, da
kuma jari.
Bayan kai tallafin ga sansanonin ‘yan gudun hijira da
tashin hankalin Boko Haram ya shafe su, hukumar ta
NEMA ta kai tallafi na musamman ga wasu da tashin
hankalin kabilanci ya raba da gidajensu a yankin
Guyuk, Lamurde da kuma jihar Taraba.
Mr. Midala Iliya Anuhu, jami’in hukumar ta NEMA mai
kula da jihohin Adamawa da Taraba, ya bayyana irin
tallafin da suka kai, kamar kayan abinci da dai
sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *