July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin sama sun yi nasara kan ‘yan bindiga a jihar Sokoto

1 min read

A daidai lokacin da Rundunar
sojin saman Najeriya ta ce ta sami gagarumar nasarori
a yakin da take yi da ‘yan ta’adda a yankin gabashin
jihar Sokoto, mazauna yankunan sun ce har yanzu ba
za’a rasa fargaba ba, domin ‘yan bindigar suna nan
kusa da jama’ar yankin.
Babban hafsan sojin saman Najeriya, Air marshall Sadiq
Baba Abubakar shi ne ya furta batun samun nasarar a
wurin bikin da rundunar sojin sama da ke jihar
Sokoton ta gudanar don taya murnar Sallah ga sojojin
da ke bakin daga a yankin.
Air marshall Sadiq Baba Abubakar, ta bakin
kwamandan rundunar dabarun kai farmaki da jirage,
AVM Olusegun Philip ya ce, aikin da mayakan saman
suke gudanar wa ya taikamaka gaya wajen dakile
ayukan ta’addanci a yankunan.
Wasu daga cikin mazauna yankunan sun shaidawa
wakilin muryar Amurka cewa, sun gudanar da bikin
sallah lafiya, ba tare da wani tashin hankali ba. Amma
sun nuna damuwarsu da fargaba, domin a cewar su
‘yan bindigar suna kusa da yankunan nasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *