June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Boko Haram Sun mutane 16 Kashe Akalla Mutane 16

1 min read

Wasu da ake kyautata zato
mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kashe akalla
mutum 16 tare da jikkata wasu 7 a jiya Lahadi a wani
hari na gurneti da aka kai a wani sansanin ‘yan gudun
hijira da ke arewacin Kamaru, a cewar Jami’an kasar.
Maharan sun jefa gurnetin ne akan wasu mutane da ke
barci a cikin sansanin a kauyen Nguetchewe, kamar
yadda magajin garin yankin Medjeweh Boukar ya fada
wa kamfanin dillanci labaran Reuters. Akwai mutane
kusan 800 a sansanin a cewar Boubakar.
Kauyen Nguetchewe dai na kusa da iyakar Najeriya da
kasar.
Mazauna yankin sun fada wa Boukar cewa mutum 16
suka mutu. A baya wani jami’in tsaro ya ce mutum 15
ne suka mutu. An kuma kai wadanda suka jikkata a
wani asibiti da ke kusa, a cewar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *