July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnonin APC sun ce zasu samar da tsaro da kansu arewa

1 min read

Gamayyar kungiyoyin gwamnonin jam’iyyar APC sun ce za su samar da mafita da za ta magance matsalolin tsaro da ya addabi Arewa maso gabashin kasar nan.
Kazalika gwamnaonin sun yi alkawarin samar da kwamitin kwararru a kowacce jiha.
Hakan na cikin jawabin da shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu ya gabatar yayin wata ziyarar jaje da suka kai wa gwamanan Jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum sakamakon hari da wasu yan ta’adda suka kai masa a baya-bayan nan.
Bagudu ta cikin jawabin nasa ya ce, akwai bukatar samar da isassun kudade da za su taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci a jihar ta Borno.
Kazalika Bagudu ya kuma ce, ziyarar ta su za ta taimaka wajen karfafawa gwamnati da al’ummar jihar Borno Gwiwa na halin fargaba da suke ciki, yana mai cewa akwai bukatar jami’an tsaron kasar nan su kara jajircewa don dakile ayyukan ‘yan tada kayar baya a kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *