July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mata sun hada gwiwa domin yakar Shugaban Kasa.

1 min read

Mata ukun da suka sadaukar da komai domin siyasa.
Svetlana Tikhanovskaya, Veronika Tsepkalo da kuma Maria
Kolesnikova sun hada kai domin su jagoranci wani kampe na zama
shugaban kasa a babban zaben Belarus da za a yi a cikin watan da
muke ciki na Agusta.
Idan har suka samu nasara to Tikhanovskaya ce za ta kasance
shugabar kasa.
Ta yanke shawarar maye gurbin mijinta Sergei Tikhanovsky bayan an
kama shi an kai shi gidan yari sannan kuma aka hana shi takarar.
Ta sha fuskantar barazana daga mahukuntan kasar a kan za a kwace
‘ya’yanta daga wajenta idan har ta ci gaba da takarar amma kuma
hakan bai sanyaya mata gwiwa ba.
Sun hada hannu da karfe tare da Veronica Tsepkalo, wadda aka
haramta wa mijinta takarar shugaban kasa da kuma Maria
Kolesnikova, mai magana da yawun dan takarar shugaban kasar da
aka kai a gidan yari Viktor Babaryko.
Manufarsu ita ce su lashe zaben 9 ga watan Agustan da za a yi a
kasar sannan kuma su kawo karshen mulkin Alexander Lukashenko
da ya shafe shekara 26 yana yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *