June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Muhammadu Buhari: Za a yi wa tsarin tsaron Najeriya garan bawul

1 min read

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ba da umurnin a sake
fasalin baki dayan tsarin tsaron kasar domin magance matsalolin da
ake fuskanta.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana
Munguno ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kammala
taron majalisar tsaron kasar a fadar Aso Rock.
A cewar Monguno, Shugaba Buhari ya bukaci manyan hafsoshin
tsaron kasar su sake dabarun tsaron kasar ta yadda za a shawo kan
matsalolin tsaro a yankin arewa maso yammaci da kuma arewa
maso tsakiyar Najeriyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *