Mutum 8 Suka Mutu a Najeriya Ranar Litinin
1 min read
Hukumar sa ido kan cututtuka
masu yaduwa (NCDC) a Najeriya ta tabbatar da cewa an
samu karin mutum 288 da suka kamu da cutar
COVID-19 a kasar abinda ya sa gaba dayan adadin ya
kai 44,129.
Hukumar ta NCDC ta bayyana hakan ne a shafin ta na
Twitter a daren ranar Litinin 3 ga watan Agusta, ta
kuma ce an samu mutum 8 da suka mutu sakamakon
cutar.
Ya zuwa yanzu, mutum 20,663 suka warke daga cutar
aka kuma sallame su daga asibiti mutum 896 kuma
suka mutu a jihohi 36 ciki har da birnin Tarayya Abuja.
Hukumar ta ce an samu sabbin alkaluman ne daga
jihohi 15 da suka hada da: Lagos (88), Kwara (33), Osun
(27), birnin tarayya Abuja (25), Enugu (25), Abia (20),
Kaduna (17), Plateau (13), Rivers (13), Delta (10),
Gombe (8), Ogun (4), Oyo (3), Katsina (1), sai kuma
Bauchi (1).