April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shoprite zasu bar Nigeria-corona

1 min read

Alamu na nuna cewa babban kantin sayar da kayayyakin nan mallakin kasar Afrika ta Kudu zai yi gwanjon kantinan da ke nan Najeriya.
Mahukuntan shagunan na Shoprite dai sun ce sun dauki wannan mataki ne sakamakon yadda ayyuka da ciniki suka tsaya cik, saboda annobar Covid-19.
Wannan dai na kunshe ne ta cikin jawabin saye-da sayarwa da kasuwanci da kamfanin ya saba fitarwa duk mako wanda kuma wannan shine karo na 53.
Kamfanin yace mafi yawa daga cikin masu zuba jari cikin harkokin kasuwancin kantunan na Shoprite sun janye saboda Covid-19 din a don haka ne ya zama wajibi su dauki wannan mataki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *