June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

za’a kuma sanya dokar kulle a jihar Kaduna

1 min read

Gwamnatin Kaduna ta ce tana duba yiwuwar sake rufe jihar saboda
tashin alƙaluman mutanen da cutar korona ke kamawa a baya-
bayan nan, “saboda mutane ba sa bin doka”.
Yayin zantawa ta musamman da BBC, Gwamna Nasir Elrufa’i ya
bayyana fargabar kada ƙaruwar annobar ta fi ƙarfin asibitocin
Kaduna bisa la’akari da ganin yadda ƙwayar cutar ke ƙara bazuwa.
Alƙaluman da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ke fitarwa a
kullum sun bayyana gano masu cutar korona 54 ranar Juma’ar da ta
gabata.
“Ranar Juma’a za ka ga mutane sun yi cunkoso, to, idan muka ce za
mu buɗe masallatan khamsus salawat wannan cunkoso za a ci gaba
da shi, ba a bin doka, ba a bin tsare-tsare,” in ji gwamna.
A cikin kwana uku na baya-bayan nan kaɗai, cutar korona ta kama
mutum 95 a jihar Kaduna, kamar yadda ƙididdigar NCDC ta nuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *