June 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Buhari ya nada Abdulmumin jibril Kofa Darakta.

2 min read

Gwamnan Jihar Kano Ganduje Ya Godewa Shugaba Buhari Saboda Mukamin Da Ya Ba Jibrin Kofa Na Babban Daraktan Gudanarwa A Hukumar Gidaje Ta Kasa

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda mukamin da ya ba Abdulmumin Jibrin Kofa na Babban Daraktan Gudanarwa Mai Kula Da Cigaban Cinikayya da Gidaje, a Hukumar Gidaje Ta Kasa.

Mukamin dai sahun farko ne na shekaru hudu. Sannan kuma ya fara ne tun daga 16 ga Watan Juli, ta wannan shekara ta 2020.

Ya ce “A madadin gwamnati da jama’ar jihar Kano ina yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda wannan mukami da ya ba wa Abdulmumin Jibrin Kofa a Hukumar Gidaje Ta Kasa na Babban Daraktan Gudanarwa. Mu na tabbatarwa da Shugaban Kasa cewa lallai an samu jajirtacce wanda zai nuna halasci a wannan muhimmin aiki da a ka ba shi.”

“Mu na masu tabbatarwa Shugaban Kasa cewa, wanda a ka ba wannan mukami zai yi iya yin sa ganin cewa manufar gwamnatin tarayya kan abinda ya shafi gidaje ta kara samun tagomashi saboda cigaban kasa da ‘yan kasa gaba daya,” in ji Gwamnan.

Sannan a yayin da Gwamnan yake karbar Kofa din, a masaukin Gwamnan da ke Asokoro a Abuja, wanda ya je domin ya yi godiya da kuma nunawa Gwamnan takardar kama aiki da a ka ba shi, Gwamna Gandujen ya shawarce shi da ya zama wakilin Kano na gari a wannan sabon waje da a ka ba shi wannan muhimmin mukami.

Kofan ya tabbatarwa Gwamnan cewa zai iya yin sa ganin cewa ya kara daga darajar jihar Kano, saboda kyakkyawan riko da zai wa aikin, wajen tabbatuwar yin aiki sahihi wanda zai kara daga likkafar gwamnatin Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *