September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Cin hanci ya sa an naɗa mataimakin shugaban kasa ministan lafiya

1 min read

An naɗa mataimakin shugaban kasar Zimbabwe Constantino
Chiwenga a matsayin sabon ministan lafiya na kasar, bayan an
kwashen kimanin wata daya ana ta rikicin cikin hanci da ya dabaibaye
ma’aikatar kan kayayyakin kariyar cutar korona.
Mista Chimwenga tsohon shugaban soji ne wanda ya jagoranci karbar
mulki daga hannun tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.
Wanda ya gada a ma’aikatar lafiyar Obadiah Moyo ya bayyana gaban
kotu a watan Yuni kan zargin cin hanci da rashawa da ake tuhumarsa
da shi, na kuɗade da suka kai dalar Amurka biliyan 20, kan wata
kwangila da aka bai wa wani kamfanin kasar Hungary wanda ake zargin
ba abi ka’idar bayar da ita ba.
An dai bayar da belin shi.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce shugaba
Mnangagwa ya lura akwai bukatar daukar matakan gaggawa kan tsarin
kiwon lafiyar kasar dangane da abin da ya shafi annobar korona.
Zimbabwe na da masu korona 4,200 kuma mutum 81 sun mutu
sakamakon cutar, amma da alamun wannan adadin da gwamnati ta
fitar zai iya zarce hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *