June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin jihar Bauchi ta yanke hukuncin rataya akan masu fyade

2 min read

Gwamnatin jihar Bauchi ta kafa wata doka da ake kira BAP wadda ta
tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da
laifin yi wa yara kanana Fyade.
Haka ma dokar ta tanadi ɗaurin rai da rai ga wanda ya yi wa babbar
mace fyade da kuma ɗaurin shekaru 20 ga wadanda suka yi wa
mace daya taron dangi.
Wannan dai na zuwa ne yayin da hukumomin ‘yan sanda a jihar suka
ce sun samu rahotannin aikata fyade har 21 a cikin wata ɗayan da ya
wuce kawai. Ko a baya-bayan nan ma ‘yan sanda a jihar sun sanar da kama wani
mutum da suke zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekaru uku fyade.
DSP Muhammad Ahmad Wakili, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar
ta Bauchi ya ce dokar tuni aka amince da ita a majalisa kuma za a
wallafa ta.
A cewarsa, tsakanin watan Yuli da Agusta sun gabatar da mutum 22
da ake zargi da aikata fyade gaban ‘yan jarida.
Ya ce sun yi hakan saboda “muna son mutane su kyamaci wannan
abin su gane cewa idan an yi wa mace fyaɗe mai da al’uma baya ne
saboda har ta gama rayuwarta da wannan (ƙyamar da ake nuna
mata).”
DSP Wakili ya ce laifin fyaɗe ba wai yarinyar da aka yi wa ya shafa
ba, laifin ya shafi ƙasa ne.
“Duk wanda muka kama ya yi fyaɗe, ba za mu yi wata-wata ba, sai
mun gurfanar da shi gaban kotu, kuma wannan (dokar) BAP ita za
mu saka ma shi a gaban kotu.” in ji DSP Wakili.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *