September 21, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jami’ar Yan sanda dake Wudil ta dage zana jarabawar shiga jami’ar

1 min read

Jami’ar ‘yan sanda dake Wudil ta ce ta dage shirin ta na yin jarrabawar shiga karo na takwas har zuwa wani lokaci anan gaba.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ASP Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.
Ndukwe ya ce tun a baya an tsara gabatar da jarrabawar shiga jami’ar a 8 ga watan da muke ciki na Agusta.
Ya kara da cewa, matakin na zuwa ne biyo bayan annobar COVID-19 da aka fuskanta a bana, da kuma sauya lokacin rubuta jarrabawar WAEC da NECO da kuma NABTEB.
Sanarwar ta kara da cewa, jami’ar za ta sanar da lokacin za’a rubuta jarrabawar anan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *