September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum 78 sun mutu sakamakon fashewar abubuwa

2 min read

Ƙarfin fashewar ya girgiza daukacin birnin sannan ya lalata gidaje da
gine-ginen da ke titunan da ke da nisan kilomitoci daga inda lamarin
ya faru.
Shugaban kasar Michel Aoun ya ce ton fiye da 2,750 na wasu
sinadirai da aka ajiye a wani wajen ajiye kayayyaki na tsawon
shekaru shida ne ya janwo wannan barna.
Shugaban zai jagoranci wani taron ministoci a ranar Laraba, sannan
ya kaddamar da dokar ta baci na tsawon makonni biyu.
Za a shafe kwanaki uku ana zaman makoki a fadin kasar tun daga
ranar Laraba.
Shugaban ƙasar Lebanon Michel Aoun ya kira wani taron gaggawa na
kwamitin tsaron ƙasar, inda shi kuma firai ministan ya ayyana Laraba
a matsayin ranar da ƙasar za ta yi zaman makoki.
Ya kuma yi magana kan abin da ya kira “wani ɗakin ajiye kaya da aka
tara sinadarai a ciki tun 2014”, amma ya ce zai bari shari’a ta dauki
mataki kan batun.
Kafofin watsa labarai na ƙasar sun nuna hotunan mutane a
ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Wani wanda ya shaida lamarin ya
bayyana ƙarar fashewar ta farko a matsayin mai gigitarwa, kuma
hotunan bidiyo sun nuna yadda fashewar ta lalata motoci da gine-
gine masu yawa.
An kuma ji ƙarar fashewar a tsibirin Cyprus mai nisan kilomita 240 a
can cikin gabashin tekun Rum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *