Za’a fara siyar da litar manfetir a Kano 150-Ipman
1 min read
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta umarci mambobin ta da su rinka siyar da man fetur lita daya akan farashin Naira dari da hamsin.
Umarnin na kunshe cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar IPMAN na jihar Kano Bashir Dan Malam ya fitar aka rabawa manema labarai.
A cewar sa matakin na zuwa ne don yin biyayya da tsarin Gwamnatin tarayya na kayyade farashin man fetur din dai-dai da yadda yake a kasuwar duniya.
Idan ba a manta ba dai, hukumar dake kula da Depo-Depo din mai ta bakin manajan bangaren kasuwanci Muhammad Bello, ta bayyana farashin man a fadin kasar nan.
Sanarwar ta bukaci mambobin kungiyar ta IPMAN da suyi biyayya da matakin hukumar, don tabbatar da cewa ba a siyar da man fetur din fiye da farashin ba.