Buhari amince da sanya dokar Lockdown na tsawon mako Hudu a fadin Nigeria.
1 min read
Buhari ya amince da tsawaita dokar kulle da mako huɗu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tsawaita dokar kullen
da aka sassauta kashi na biyu da makonni huɗu.
Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin da shugaban
ƙasa ya kafa na yaƙi da cutar korona Boss Mustapha ne ya bayyana
hakan a Abuja yayin wani bayani ga ‘yan jarida kan cutar.
Wannan ne dai karo na uku da ake tsawaita kashi na biyu na sassaucin
dokar kullen a faɗin ƙasar.
Akwai shawarwari da sakataren gwamnatin ya bai wa shugaban ƙasar
kan ci gaba da sassaucin wannan doka, sai dai ba a fito da bayanai kan
shawarwarin ba.