Gwamnatin Jihar kano ta gudanar feshin maganin sauro a Makarantu Masu zaman kansu
2 min read
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci shugabannin makarantu masu zaman kansu dasu saukakawa iyaye wajen biyan kudin makaranta duba da yanayin da ake ciki na Corona.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake kaddamar da feshin magani a makarantun sakandaren jihar nan na gwamnati da masu zaman kansu.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje Wanda mataimakin gwamnan Kano kuma shugaban kwamitin Kar ta kwana kan yaki da Corona Nasir Yusif Gawuna ya wakilta ya ce ya zama lallai a yiwa makarantun feshin maganin don kare dalibai daga cutar Corona.
Gawuna ya Kara da ana samun nasara matuka wajen yaki da Corona duba da yadda kwanaki biyar da suka wuce baa samu mutum ko daya daya kamu da Corona anan Kano ba.
Ya kuma ce gwamnan Kano ya umarci da a fara feshin da makarantu masu zaman kansu don su ma su San gwamnatin na tare dasu.
Da yake jawabi shugaban kungiyar masu makarantu masu zaman kansu reshen jihar Kano Alhaji Muhammad Malam Adamu bayyana Jin dadinsa yayi bisa ga wannan taimako da gwamnati tayi musu duba da halin da suka tsinci kansu na rashin kudi saboda annobar ta Covid 19.
Anasa bangaran kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dr Kabir Ibrahim Getso na cewa makarantun gwamnati 199 zaa yiwa feshin maganin yayin da makarantu masu zaman 329 zaa yiwa feshin maganin a fadin jihar ta Kano.