September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

ISIS da Al-Qaeda ‘sun kutsa yankin arewa maso yammacin Najeriya’

1 min read

Amurka ta bayyana cewa kungiyar ISIS da Al-Qaeda sun soma
kutsawa zuwa yankin arewa maso yammacin Najeriya.
A watannin da suka wuce an samu karuwar hare-hare a Kaduna da
Katsina da Sokoto da Zamfara da kuma wasu jihohin yankin.
A taron manema labarai, kwamandan dakarun Amurka na
musamman a Afrika, Dagvin Anderson ya kara da cewa kungiyar Al-
Qaeda kuma na kara fadada rassanta a yankunnan kasashen
yammacin Afrika.
wajen Amurka, Anderson y ace Amurka za ta ci gaba da hada gwiwa
da Najeriya domin musayar bayanan sirri.
A cewarsa hare-haren Al-Qaeda sun janwo rufe makarantu fiye da
9,000 kuma 3,000 daga ciki a kasashen Mali da Burkina Faso.
“Muna tattaunawa da Najeriya kuma za mu ci gaba musayar
bayannan sirri domin kara fahimtar ayyukan masu tsattsaurar ra’ayi,”
in ji Anderson.
“Hakan na da matukar mahimmanci gannin yadda kungiyar ta yi
barna a jihar Borno kuma a yanzu ta soma samun gindin zama a
yankunan arewa maso yammacin Najeriya.” Anderson ya ce idan ana son taimakon kasashen waje yayi tasiri a
yaki da ta’addanci a Najeriya dole ne gwamnatin kasar ta shiga
sawun gaba wajen murkushe kungiyar.
“A kan batun Najeriya, kasar na da mahimmanci a yammacin Afrika.
Akwai bukatar gwamnati ta shiga gaba domin zubarar da yunkurin
yaki da kungiyar”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *