April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Labari da dumi duminsa matasa na gudanar zanga-zanga a jihar Katsina

1 min read

Ba wannan ne karon farko da matasa ke zanga-zanga a jiar ta
Katsina ba sakamakon tabarbarewar tsaron jihar.
A farkon watan Yuni mazauna kauyen ‘Yantumaki sun gudanar da
zanga-zanga kan tabarbarewar tsaron da yankin ke fama da shi.
Bayanai sun nuna cewa matasan yankin sun harzuka ne bayan wasu
‘yan bindiga sun kai hari a kauyen inda suka sace wani malamin
asibiti da diyarsa.
Mazauna jihar na dora alhakin wadannan hare-hare kan gazawar
hukumomi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa hukumomin tsaron
kasar umarnin kaddamar kakkabe ‘yan bindiga da suka addabi
jama’a a jihar ta Katsina sai dai har yanzu ana ci gaba da fuskantar
matsalar hare-haren ‘yan bindigar.
A watan jiya, uban kasar Batsari da ke jihar ta Katsina ya shaida wa
BBC cewa akwai kimanin mata 600 da aka bari da marayu
sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da suka kashe mazajensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *