June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutane 927 suka mutu a sakamakon annobar corona a Nigeria.

2 min read

Mutane 314 sun warke daga cutar Covid-19 jiya Laraba a fadin kasarnan, cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta sanar a daren Alhamis ta shafinta na Twitter cewa, wannan kari da aka samu yakai adadin wadanda suka warke daga cutar a kasar nan zuwa mutane 32,165.
A cikin sanarwar NCDC ta ce, an samu karin mutane 457 da suka kamu da cutar Corona a jihohi 20 na kasarnan da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Haka kuma an samu karin mutane 17 da cutar tayi ajalinsu, wanda hakan ke nufin zuwa yanzu cutar Corona ta hallaka mutum 927 tun bayan bullarta a kasar.
Zuwa yanzu mutane 44,890 NCDC ta tabbatar sun kamu da cutar Corona a Najeriya.
A nan Kano ma, gwamnatin Kano ma ta tabbatar da cewa an samu karin mutum 1 da ya kamu da cutar a jiya Laraba, sannan kuma mutum 5 sun warke daga cutar.
Ma’aikatar lafiya ta Kano ta sanar a shafinta na Twitter cewar, hakan na nufin adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da Corona a Kano zuwa yanzu ya kai 1,559, daga ciki an sallami 1,275 bayan da suka warke daga cutar, sai mutum 53 da cutar tayi ajalinsu a jihar.
A jihar Kaduna kuwa gwamnatin jihar ta ce an samu karin mutum 9 dauke da cutar, sannan an sallami karin mutum 9 da suka warke a jiya Laraba.
Zuwa yanzu mutane 1,297 ne suka warke daga Corona a jihar cikin mutane 1,507 da aka tabbatar sun kamu da cutar, sai mutum 12 da cutar ta hallaka a jihar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *