April 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sakacin gwamnatine wajen mutuwar al’ummar lebanon

2 min read

Mutane a birnin Buirut sun nuna fushinsu ga gwamnati kan cewa
sakacinta ne ya janyo fashewar sinadirai a ranar Talata.
Shugaba Michel Aoun ya ce ton 2,750 na sinadarin ammonium nirate
da aka ajiye ba tare da bin tsarin kariya ba.
Fashewar ta janyo mutuwar mutum akalla 135 tare da jikkata fiye da
4,000 kuma yanzu haka dokar tabaci na makonni biyu a kasar.
Ammonium nitrate sinadirai ne da ake amfani da su wajen yin takin
zamani domin noma sannan ana amfani da su wajen kera abubuwan
fashewa.
Shugaban zai jagoranci wani taron ministoci a ranar Laraba, sannan
ya kaddamar da dokar ta baci na tsawon makonni biyu.
Za a shafe kwanaki uku ana zaman makoki a fadin kasar tun daga
ranar Laraba. Ministan harkokin cikin gidan na ƙasar ya ce binciken farko ya nuna
cewa wani sinadari ne da aka ajiye a cikin tashar jirgin ruwan ya
fashe.
Firai minista Hassan Diab ya ce za a hukunta waɗanda suka yi
sakacin aukuwar wannan iftila’in:
“Ba za a kyale wannan lamarin ya wuce ba a dauki mataki ba.
Dukkan wadanda suke da alhakin wannan iftila’in za su ɗanɗana
kuɗarsu. Wannan alkawari ne na ɗauka ga waɗanda suka sadaukar
da rayukansu, da waɗanda aka jikkata, kuma wannan ya kasance
alƙawari da ƙasar nan ta ɗauka.”Shugaban ƙasar Lebanon Michel Aoun ya kira wani taron gaggawa na
kwamitin tsaron ƙasar, inda shi kuma firai ministan ya ayyana Laraba
a matsayin ranar da ƙasar za ta yi zaman makoki.
Ya kuma yi magana kan abin da ya kira “wani ɗakin ajiye kaya da aka
tara sinadarai a ciki tun 2014”, amma ya ce zai bari shari’a ta dauki
mataki kan batun.
Kafofin watsa labarai na ƙasar sun nuna hotunan mutane a
ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Wani wanda ya shaida lamarin ya
bayyana ƙarar fashewar ta farko a matsayin mai gigitarwa, kuma
hotunan bidiyo sun nuna yadda fashewar ta lalata motoci da gine-
gine masu yawa.
An kuma ji ƙarar fashewar a tsibirin Cyprus mai nisan kilomita 240 a
can cikin gabashin tekun Rum. Wanan iftila’in ya zo wa Lebanon a lokacin da ta ke cikin mawuyacin
hali, kamar matsananciyar matsalar tattalin arziki da ta rarraba
kawunan ‘yan kasar, da kuma zaman ɗar-ɗar da ake yi kan yanke
hukuncin da wata kotu za ta yi wa wadanda suka kashe tsohon firai
ministan kasar Rafik Hariri a 2005.
Wata kotun Majalisar Ɗinkiun Duniya ce ke shirin yanke hukunci
game da shari’ar, wadda ake zargin wasu mutum huɗu da aikata
kisan ta hanyar tashin wani bam a mota.
Dukkanin mutum huɗun ‘yan ƙungiyar Hezbollah ne wadda ke samun
goyon bayan Iran, wadda kuma ta sha musanta zargin hannunta a
ciki. Ranar Juma’a za a yanke hukuncin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *