June 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin Nigeria sun mai da martani ga Gwamnan Borno

2 min read

Hedikwatar tsaron Najeriya ta musanta zargin da aka yi cewa sojoji
ne suka kai hari ga ayarin motocin gwamnan jihar Borno Babagana
Umara Zullum.
A cewar sojin, ‘yan Boko Haram ne suka kai hari, ba kamar yadda ake
cewa zagon kasa ne daga wajen jami’an tsaro.
Mako guda kenan cif da wasu masu dauke da makamai suka bude
wuta kan ayarin gwamnan lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa
garin Baga domin wata ziyarar aiki.
Sai da aka shafe mako daya kafin rundunar sojin kasar kafin su
mayar da martani kan wannan zargin da suka kira mai nauyi a bainar
jama’a, duk da yadda gwamnan ya sha fada yana nanata zargin nasa.
Yayin wata hira da gidan talabijin din Channels mai zaman kansa a
Najeriya, babban jami’in watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo
Janar John Enenche ya ce sakamakon binciken da suka yi kan
bidiyon harin, ya nuna cewa mayakan Boko Haram ne suka kai shi,
ba sojojin kasar ba kamar yadda gwamma Zulum yake zargi ba.
“Don haka mun yi bincike kan bidiyon nan take kuma mun gano
cewa sashen tsara dabarun yaki bai da hannu a ciki,”, in ji Manjo
Janar Enenche.
Ya kara da cewa “Mun yi wa bidiyon nazari na tsanaki. Ko daga karar
harbe-harben, za ka fahimci cewar ba karar irin makaman da muke
amfani da su bane. Idan ka jima kana fada da abokin gaba to za ka
kai matakin da duk wasu halayensa za ka fahimcesu”.
Janar Enenche ya kara da cewa masu ruwa da tsaki a lamarin za su
dauki mataki kan wannan batun.
‘Zulum ya fusata’
A ranar 30 ga watan Yuli bayan an kai harin, gwamnan jihar Borno ya
nanata cewa ƙoƙarin murƙushe ƙungiyar Boko Haram na shan zagon
ƙasa daga wani rukuni na jami’an tsaron ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *