June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Adadin waɗanda suka mutu a Beirut ya kai 154 Adadin

1 min read

waɗanda suka mutu sakamakon fashewar sinadarai a Beirut
babban birnin Lebanon ya kai 154.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ne ya ruwaito ministan lafiya na
ƙasar inda ya ce akwai mutum 120 da suna cikin wani hali.
Hamad Hassan ya bayyana cewa da dama daga cikinsu suna buƙatar
tiyata ta gaggawa musamman wadanda gilas ya yanka su.
Wannan lamarin na tashin hankali ya faru ne a Beirut babban birnin
ƙasar wanda ya jikkata mutum sama da dubu biyar da kuma ɓarnar da
ba a iya kiyastawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *