July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kashe mutane 33 a Zangon-Kataf a Kaduna

1 min read

A kalla mutane 33 sun rasa rayukansu akasarinsu mata
da kananan yara bayan wasu ‘yan bindiga sun kai sabon
farmaki a kauyukan yankin Atyap da ke Karamar Hukumar
Zangon-Kataf ta jihar Kadunan Najeriya. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta rawaito cewa, an kaddamar da jerin
hare-haren ne da misalin karfe 11 na dare a ranar Laraba da kuma
karfe 1 na dare a ranar Alhamis a kauyukan Apyiashyim da
Atak’mawai da Kibori da Kurmin Masara da ke karkashin masarautar
Atyap a Zangon Kataf.
Wata majiya ta bayyana cewa, an kai farmakin ne a daidai lokacin da
ake tafka ruwan sama mai karfin gaske, yayin da tsagerun suka
karkashe jama’a tare da raunata wasu da dama duk da cewa akwai
dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *