June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Bibiyyar ayyuka na daya daga cikin hanyoyin magance annobar Covid 19-Farfesa Kurawa

1 min read

Shugaban Kwalejin Fasaha ta jihar Kano wato Polytechnic Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, ya ja hankalin daukacin ma’aikatan Kwalejin wajen ci gaba da yin biyayya ga dokokin dakile annobar COVID-19.
Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya bayyana hakan ne ta cikin sakon kammala bikin Sallar Layya lafiya da jami’in hulda da jama’a na Kwalejin Garba Isma’il Fagge ya aikewa manema labarai.
Ya ce shakka babu Kwalejin ta bada ta ta gudunmawar wajen yaki da wannan annoba, wajen kirkirar na’urorin da za su saukaka wajen tsaftace hannaye, don cika ka’idojin kwararru kan kiwon lafiya.
Ta cikin sakon dai Farfesa Atiku Kurawa, na cewa ya zama wajibi al’umma su maida hankali wajen lafiyar su, da kuma yin hobbasa wajen tallafawa kokarin Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje na yaki da annobar ta COVID-19.
Har ila yau Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya taya daukacin al’ummar musulmin jihar Kano murnar kammala bukukuwan Sallah babba cikin kwanciyar hankali, da kuma Gwamna Ganduje da sauran mukarraban Gwamnatin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *