July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Buhari ya amince da Ize-Iyamu a matsayin ɗan takarar APC a Edo

1 min read

Gwamnan jihar Yobe kuma Shugaban jam’iyyar APC na riƙo Mai Mala
Buni ya shaida cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince
da Fasto Osagie Ize-Iyamu a matsayin ɗan takarar gwamna a jam’iyyar
APC a jihar Edo.
A wani hoto da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan kafafen sada
zumunta na zamani Bashir Ahmed ya wallafa a shafinsa na Twitter, an
ga shugaban ƙasar yana miƙa wa Mista Iyamu tutar jam’iyyar APC.
Ɗan takarar kuma ya yi watsi da zargin da ake yi cewa ‘yan majalisar
jihar 14 a ranar sun yi zama a gidansa domin tsige kakakin majalisar
Edo domin zaɓen sabo.
A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya koma
jam’iyyar PDP daga APC sa’annan kuma Osagie Ize-Iyamu ya koma
APC daga PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *