April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Champions League: Real Madrid na tsaka mai wuya a wasa tsakaninta da Man City

2 min read

Idan ana maganar gasar Champions ce a Turai, idan Real Madrid ta
ɗaga hannu babu wata kungiya da ta isa ta lankwasa mata.
Amma idan ana maganar wasa tsakaninta da Man City, za a iya cewa
da karfin gwiwa City za ta fito, idan aka yi la’akari da wasanni ukun
da aka buga a baya-bayan nan, biyu duka an yi canjaras ne daya
kunnen doki, da kuma wanda aka yi kurman diro.
Sai wasan farko da aka yi a na siri daya kwale na Champions din
wannan shekarar gabanin annobar korona, wanda Real Madrid ta sha
kashi a hannun City da 2-1.
Matsalolin da Real Madrid ke fuskanta
Matsalar farko an doke Madrid 1-2 har gida, wanda kuma ita ta fara
cin kwallo kafin daga baya a farke a kara mata.
Yanzu kuma za ta je Ingila gidan Manchester City kuma har sai ta ci
kwallo biyu babu ko daya ko uku da daya kafin ta iya cin ye City.
Sergio Ramos ba zai buga wasan ba saboda katin da aka ba shi a
wasan da aka buga na farko a Santiago.
Real Madrid ta rage kwarjini tun bayan tafiyar Cristiano Ronaldo
zuwa Juventus.
Yawan wasannin da Manchester City ta yi nasara a cikinsu a
Champions wani abu ne da ake ganin zai iya yiwa Real Madrid
mummunan tasiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *