July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnonin Arewa sun yi tir da hare-haren kudancin Kaduna

2 min read

Kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi alawadai da harin baya-
bayan nan da aka kai Kudanci Kaduna wanda ya yi ajalin mutane 22 a
ranar Laraba. Wanda har yanzu ba a kai ga kama ko daya daga cikin
wadanda suka kai harin ba cikin kauyuka hudu na karamar hukumar
Zangon Kataf da ke kudancin jihar.
Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, shugaban kungiyar gwamnan
jihar Plateau Simon Bako Lalong ya ce ci gaba da kai hare-haren da ake
yi a kauyukan duk da cewa gwamnatin jihar Kaduna da sauran jami’an
tsaro na iya kokarinsu na ganin sun kawo karshen ta shin hankalin da
kowa ke ala wadai da shi na nuna har yanzu da sauran aiki a gaba.
Wannan harin da aka kai na bayan nan da aka kai kauyen Atyab da ya
shafi mutanen da babu ruwansu, ba kawai bakinciki da bacin rai ya
haifar ba, har ma da kokarin mayar da hannun agogon baya da ya yi na
gwamnatin jihar Kaduna na samar da zaman lafiya a jihar.
Ya ce ” Abin bakin ciki ne wannan kai hari kan mutanen da ba sa dauke
da makamai domin ba su da mataimaki, abin alwadai ne da nadama.
Muna kira ga jami’an tsaro su tashi tsaye wajen bankado wadannan
masu laifi, kuma muna rokon jama’a da su taimaka wajen bayar da
bayanan da za su kai ga kama wadannan mutane.”
Kungiyar ta jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwansu da kuma
gwamnan jihar Nasir el-Rufa’i, suna fatan ganin wannan rikici ya zo
karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *