July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hatsarin jirgin sama ya rutsa da mutum 191 a ƙasar

1 min read

Wani jirgin sama a Indiya ya yi hatsari ɗauke da mutum 191 a wani
filin jirgi da ke jihar Kerala a kudancin ƙasar.
Jirgin mai suna Air India, ya taso ne daga Dubai wanda yayin sauka
ya zame daga titin jirgi inda ya rabe biyu, in ji hukumomi a Indiya.
Rahotanni sun bayyana cewa masu aikin ceto na nan na aiki domin
ceto waɗanda ke cikin jirgin.
An dai tabbatar da mutuwar mutum 16, ciki har da direban jirgin. Wani mai magana da yawun kamfanin jirgin ya bayyana cewa
fasinjoji da dama sun samu rauni.
Kamfanin jirgin ya bayyana jirgin na ɗauke da fasinjoji 184 – ciki har
da yara 10 da kuma ma’aikatan jirgin bakwai da kuma direbobin
jirgin biyu.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na dare a ƙasar, yayin da
ake ruwan sama mai ƙarfi.
A watan Mayun 2010, mutum 158 suka mutu bayan jirgin Air India ya
yi hatsari a filin jirgin sama na Mangalore a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *