July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

INEC ta samar da shafin da za a rika bibiyar zaɓe kai tsaye

1 min read

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce ta samar da wani shafin intanet da
zai bai wa ‘yan kasar damar bibiyar kirga kuri’un zabe daga gida.
Cikin wani sakon Twitter da ta wallafa a shafinta hukumar ta ce an
samar da shafin ne domin karfafa gaskiya a harkokin zabe da dakile
wuru-wuru da kuma tabbatar da an yi komi bude.
INEC ta ce tana sane da cewa da yawa daga ‘yan kasar na da shakku
kan yadda ake gudanar da harkokin zabe, kuma suna nuna wa a fili. Im
da ta ce a wasu lokutan ma akan cin zabe da kuri’un da suka wuce
wadanda aka kada yayin zaben.
INEC ta ce ta samar da wannan shafi ne domin kawo karshen wannan
abu.
Sai dai hukumar ta ce babu tsarin yadda ake tattara sakamakon zabe a
wannan ci gaba da aka samu, tattara sakamakon zabe zai ci gaba da
kasancewa kamar yadda tsarin doka ya tanadar.
Za a fara amfani da wannan ci gaba ne a zaben cike gurbi da za a yi a
jihar Narasawa a ranar Asabar mai zuwa ta 8 ga watan Agustan 2020.
Za a kara amfani da wananan shafi a zaben Jihar Edo da ke biya masa
baya wanda zaa gudanar a watan satumba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *