July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kasosa ta dakatar da tarukan data saba gabatarwa-Covid

1 min read

Shugaban kungiyar daliban Kwalejojin Kimiyya na jihar Kano da Jigawa (KASSOSA) Alhaji Mustapha Nuhu Wali (mni), ya sanar da cewa kungiyar ta janye tarukan da ta saba yi na ajujuwa a wani mataki na dakile yawaitar cunkoso na jama’a.
Alhaji Mustapha Nuhu Wali (mni) ya bayyana hakan ne ta cikin sakon taya murnar Sallah da Jami’in hulda da jama’a na kungiyar Aminu Gidado Yusha’u ya fitar, ga dimbin mambobin KASSOSA dake fadin Najeriya.
Ta cikin sakon Sallar Idin layya, Mustapha Wali ya jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwa da abokan arziki a tsawon lokaci da aka yi ta fama da annobar cutar COVID-19, inda yayi fatan samun rahmar Allah a gare su.
Ya kuma bukaci mambobin KASSOSA a ko ina suke da su kasance suna dabbaka matakan kariya na dakile yaduwar annobar COVID-19.
Alhaji Mustapha Nuhu Wali (mni) ya kuma ja hankalin al’umma da su rubanya addu’o’in da suke yi, da kuma ci gaba da siffanta da halaye na kwarai da suka kasance a ciki tsawon kwanaki goman farko na Zul Hijja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *