June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Maleriya za ta iya kashe mutum 779,000 saboda karancin gidan sauro’

1 min read

Bincike ya nuna cewa rarraba gidan sauro a nahiyar Afrika zai iya rage
mace-macen da cutar Maleriya ke haddasawa da kusan kashi 50 cikin
100.
Akwai damuwa kan cewa annobar korona ta kawo cikas ga rabon da
aka saba yi na gidan sauro a nahiyar.
Ya kamata a ce an rarraba gidan sauro kusan miliyan 228 a ƙasashen
Afrika.
Sai dai wata makaranta a Birtaniya wato Imperial College ta yi
hasashen cewa mutanen da Maleriya za ta kashe a wannan shekarar
zai ninka sau biyu kan yadda aka saba samu a baya muddin aka samu
tsaiko wurin ɗaukar matakan kariya.
Binciken ya nuna cewa akwai yiwuwar cewa kusan mutum 779,000
cutar Maleriya za ta kashe cikin shekara guda .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *