Ambaliya Ta Jefa Al’ummar Somalia Cikin Halin Kakanikayi
2 min read
Hukumar kula da ‘yan gudun
hijira ta Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ta ce ambaliyar
tayi sanadiyar karancin abinci da ya kai ga barkewar
cututtuka masu kisa kana ya kara fargabar karin
yaduwar coronavirus a cikin kasar.
Sama mutum dubu dari da hamsin da ambaliyar ta
rutsa dasu sun rasa mtsugunai a karshen watan Yuni,
ciki har da mutum dubu 23 da suka rasa muhallan su a
makon da ya gabatan nan, a cewar jami’ai. Masu
hasashen yanayi sun ce har yanzu da sauran rina a
kaba. Sun yi hasashen cewa akwai ruwa kamar da
bakin kwarya da kuma ambaliya mai munin gaske da
za a ci gaba da gani a wasu yankuna har izuwa wani
lokaci kana zai addabi rayuwar dubun dubatar mutane
kuma ya raba su da matsugunan su.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan gudun hijiran ta
MDD, Charlie Yaxley ya yita fadar cewa sababbin
wadanda suka rasa matsugunan su, suna wani wurin
mai yawan mutane, wasu matsugunai mara kariya
dake fama da yanayi mara kyau. Ya ce iyalai na
huskantar barazanar karuwan miyagun ayyuka kamar
fashi da fyade.
Sai dai Yaxley ya ce ba a samu wani labarin barkewar
coronavirus mai yawa ba amma ya fadawa Muryar
Amurka lamarin ya yi muni. Ya ce mutane basu samun
ruwa mai tsafta, cunkuso a sansani yana hana nesanta
da juna kana babu isasshen ban-daki.