June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An yi waje da Real Madrid da kuma Juventus 7 Agusta 2020

1 min read

Manchester City ta kammala aikin da ta soma a cikin watan
Fabarairu inda ta doke Real Madrid a gasar zakarun Turai.
City ta casa Real da ci biyu da daya a wasan da suka buga a Etihad,
inda Sterling da Jesus suka ci kwallo sai kuma Benzema ya farkewa
Real kwallo daya.
‘Yan wasan Pep Guardiola za su hadu da Lyon a zagayen gabda na
kusa da karshe.
Wannan rashin nasarar it ace ta farko da Zinedine Zidane a zagaye
na biyu a matsayin koci a gasar zakarun Turai. Juventus da Lyon
A daya wasan da aka buga a ranar Juma’a da daddare, kungiyar Lyon
ta fitar da Juventus daga cikin gasar duk da cewa Ronaldo ya zuwa
kwallo biyu a wasansu.
A ranar Asabar, Barcelona za ta dauki bakunci Napoli sai kuma
karawa tsakanin Bayern Munich da Chelsea.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *