June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Bankin Duniya zai bai wa Najeriya naira biliyan 43

1 min read

Bankin Duniya ya amince ya bai wa Najeriya tallafin dala miliyan 114.28
– kwatankwacin naira biliyan 43 – domin yaƙi da annobar korona
musamman a matakin jihohi, a cewar rahoton kamfanin dillancin
labarai na NAN.
A cewar wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a, dala miliyan
100 za ta fito ne daga ƙungiyar International Development Association
(IDA), sai kuma miliyan 14.28 da za ta fito daga sashen Pandemic
Emergency Financing Facility.
Ta ce Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta bayar da lamuni ga jihohi 36
na ƙasar ciki har da Abuja ta hanyar tsarin yaƙi da annobar da aka yi wa
laƙabi da COVID-19 Preparedness and Response Project (CoPREP).
Ta ƙara da cewa shirin zai taimaka matuƙa a matsayin ɗaukin gaggawa
da zai daƙile bazuwar cutar a tsakanin al’umma.
Wakilin Bankin Duniya a Najeriya, Mista Shubham Chaudhuri ya ce:
“Najeriya ta duƙufa wurin daƙile yaɗuwar annobar korona, sai dai akwai
buƙatar a ƙara ƙaimi sosai musamman a matakin jihohi, waɗanda su
ne kan gaba a yaƙi da cutar.
“Shirin zai taimaka wa jihohi da abin da suka fi buƙata na kayan aiki da
kuɗi domin ƙarfafa gwiwarsu wurin yaƙi da annobar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *