June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Harin bam ya kashe mutum 14 a barikin sojan

1 min read

Wani hari da aka kai kan sansanin sojoji a Mogadishu, babban birnin
Somalia ya yi ajalin aƙalla mutum takwas tare da jikkata wasu 14.
Waɗanda suka shaida lamarin sun shaida wa kafafen yaɗa labarai a
ƙasar cewa wata mota ce da aka cika ta bamabamai ta tashi ginin,
wanda ke kusa da filin wasan ƙwallon ƙafa.
An jiyo ƙarar fashewar mai ƙarfin gaske a ɗaukacin birnin.
Ƙungiyar masu ikirarin jihadi ta al-Shabab ta ce ita ta kai harin. Ta
sha kai harin bam, inda take harar jami’an tsaro da manyan jami’an
gwamnati. Kanar Ahmed Muse ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AP
cewa fashewar ta faru ne a mashigar barikin soja na 12th April,
wanda ke kusa da wani sabon filin ƙwallo da aka buɗe a unguwar
Warta-Nabadda.
A watan Yunin da ya gabata aka buɗe filin wasan, wanda ake yi wa
kallon wata hanya ce ta farfaɗowar da birnin ya yi bayan kasancewa
a cikin rikici na tsawon shekaru.
Halima Abdisalan, wata uwa da ke zaune a kusa da inda lamarin ya
faru, ta faɗa wa Reuters cewa sojoji sun buɗe wuta jim kaɗan bayan
fashwar. “Mun shige cikin gida cikin firgici,” in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *