July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar Yan jaridu ta Jihar Kano ta umarci Gwamnatin Kano ta biya yan fensho kudadensu.

1 min read

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta biya tarin bashin kudaden ariya-ariya da garatuti da ‘yan fansho a jihar ke binsu na tsawon watanni.
Hakan na cikin wata sanarwar ce ta hadin guiwa da shugaban kungiyar ta NUJ reshen jihar Kano, Abbas Ibrarim da sakataren kungiyar, Abba Murtala suka fitar, jim kadan bayan kammala taron kungiyar a yau Asabar.
Tun a watan Yunin da ya gabata ne shugaban kwamitin amintattu da ke kula da asusun ‘yan fansho na jihar Kano, Alhaji Sani Gabasawa ya bayyana cewa, kudaden ‘yan fansho da gwamnatin ta gaza biya ya kai sama da naira biliyan ashirin.
Sanarawar ta bukaci gwamnatin da tayi duba kan halin da ‘yan fansho ke ciki na rashin biyan su kudaden su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *