June 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Labarina Series: Ma’anar mai hakuri yakan dafa dutse ya sha romonsa

2 min read

Kallo ya koma sama, wato shaho ya suri giwa sama kamar yadda
yake zarar dan tsako. Lallai Bahaushe ya yi hikima da fadin haka,
domin dan tsako kadai shaho zai iya sura.
Kusan wata guda ke nan, tashar talabijin ta Arewa24 ta fara nuna
wani shirin fim mai suna ‘Labarina’ wanda rubutu ne na wani labari
wanda fitaccen marubuci Ibrahim Birniwa ya kago.
Hankali ya karkata ne saboda Arewa24 sun saba nuna sababbin
shirye-shirye da suke fito da sababbin jarumai, sai shahara da
kwarewa da kayan aikin zamaninsu da kuma iya karkatar da hankalin
matasa, maza da ‘yan matan cikinsu.
Abu na biyu wajen karkatar matasan ko a tsakankanin marubuta ita
ce, shaharar marubucin wajen rubutun labari mai rike mai kallo
wajen kawo rikita-rikitar da ke sakawa mai kallo son ganin ya za a
karke ko ya za a warware a ko yaushe.
Abin da ya ja hankalina a kan yin wannan rubutun shi ne, tun a kashi
na farko wasu masharhanta suka nuna karewar labarin – wanda
maudu’insa shi ne juriya da hakuri – da watakila kashi daya kawai aka
nuna daga kashi 12 ko 13 ko wajejen hakan da shi ne zango daya
(season one) a fim mai dogon zango (series film).
Sun fadi hakan ne domin wani abin takaicin da ya yi barazanar
faruwa a kan babbar tauraruwar shirin.
Sai dai shirin na biyu ya nuna lallai labarin ya tafi da masu wannan
hasashen, domin hakan ba ta faru ba. Da ma ai sani ko camkar abin
da zai faru ka iya zama nakasu ga marubuci, domin kunshiyar labarin
da sako ko manufa ko sarrafa jigonsa na hannunsa kacokam, kuma
rashin sanin me zai faru da jiran abin da zai faru din shi ne ke jan
mai kallo ya ci gaba da yin kallon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *