March 17, 2025

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

mulki ya koma Kudancin Najeriya a 2023 – El-Rufai

2 min read

Gwamnan jihar Kaduna a Najeriya ya nemi a miƙa wa yankin
kudancin ƙasar mulki a shekarar 2023 bayan wa’adin mulkin
Shugaba Muhammadu Buhari.
Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana haka ne cikin wata hira da
yayi da BBC.
“Idan ka kalli yadda nake, ba na ɗaukar mutum yayi aiki tare da ni
domin shiyyar da ya fito. Cancanta na ke dubawa, ina duba wanda
idan aka ba shi amanar jama’a zai riƙe ta yadda ya kamata.”
Ya kuma ce, “A siyasar da ake yi a Najeriya, akwai tsarin da ake bi na
karba-karba, inda kowa ya amince cewa idan arewa ta yi mulki
shekara takwas, kudu za ta yi mulki shekara takwas.”
Ya ce duk da ba a rubuta tsarin karɓa-karɓan a tsarin mulki ba,
amma kowane ɗan siyasa a ƙasar ya san da shi.
‘Shi yasa na fito na ce bayan Shugaba Buhari ya yi shekara takwas,
ka da wani ɗan arewa ya nemi muƙamin. A bar ƴan kudu suma su
sami shekara takwas.”
Da aka tambaye shi ko da gaske yana da ra’ayin tsayawa takarar
shugabancin Najeriya, sai ya ce:
“Ana cewa ina son shugaban ƙasa tun ina ministan Abuja, amma ba
na so. Wannan shirme ne.”
Ya kuma ci gaba da cewa Allah shi ke bayar da shugabanci, “ko kana
so, ko ba ka so yana iya ba ka. Amma ni ban taɓa neman
shugabancin Najeriya ba kuma babu wanda zai ce na taɓa nema.”Batun rufe kasuwannin Kaduna
Tun da cutar korona ta bayyana a Najeriya, gwamnatoci sun ɗauki
matakan killace al’umominsu a gida inda har ta kai sun kulle
makarantu da wuraren aiki da kasuwanni.
A jihar Kaduna, duk da gwamnatin jihar kaduna ta sassauta matakan
kullen da ta saka wa al’umar jihar, har yanzu ba ta buɗe wuraren
ibada da kasuwanni da makarantu ba.
Wannan ne ya sa ƴan kasuwa ke ƙorafe-ƙorafe kan batun, suna cewa
matakin gwamnan jihar na iya kassara su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *